Home Labarai An ƙara tsaurara matakan tsaro a Sokoto

An ƙara tsaurara matakan tsaro a Sokoto

148
0

Hukumomin tsaron Nijeriya na ƙara tsaurara sintiri a ƙauyuka da dama na ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto, tun bayan da ƴan bindiga suka kashe kimanin mutane 74 a cikin mako guda.

Mazauna yankunan sun shaidawa Daily Trust cewa jami’an tsaron da suka haɗa da sojoji da ƴan sandan kwantar da tarzoma na zagaye da yankunan don tabbatar da tsaro.

Suka ce jami’an na sa ido a ƙauyukan Garki da Ɗan Aduwa, inda kusan mutanen ƙauyen sun gudu zuwa cikin Sabon Birni.

Saidai mazauna yankin sun yi kira ga hukumomi da su share dazukan da ke zagaye da ƙauyukan, waɗanda suka ce nan ne maɓoyar ƴan bindigar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply