Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta ce sama da jami’an tsaro 10,000 da suka hada da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro ne za su kula da zaben kananan hukumomin a jihar Kano.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa ‘yanjarida a Kano dangane da zaben ranar Asabar din nan cewa akwai ‘yansandan 7,251 sai sauran jami’an tsaro 2,000.
Ya lissafto sauran jami’an tsaron da suka hada da kwastan, “civil defence” Immigration”, da jami’an tsaron gidan yari.
