Home Addini An ba da hutu a Kano don bikin murnar shekarar musulunci

An ba da hutu a Kano don bikin murnar shekarar musulunci

175
0

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Alhamis 20 ga watan Agusta a matsayin ranar hutu domin murnar bikin sabuwar shekarar musulunci ta 1442.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan watsa labaran jihar Malam Muhammad Garba a Kano.

Sanarwar ta ce gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci musulmai da su yi amfani da lokacin bukukuwan sabuwar shekarar wajen yin addu’ar samun zaman lafiya da cigaban jihar.

Ganduje ya yi addu’ar neman daukin Allah kan matsin tattalin arziki da ake fuskanta wanda cutar corona ta haifar.

Sannan ya yi kira ga jama’a su ji tsoron Allah a dukkan al’muransu kuma su zauna lafiya tsakanin su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply