Home Coronavirus An bayana lokacin da Nijeriya za ta samu rigakafin Covid-19

An bayana lokacin da Nijeriya za ta samu rigakafin Covid-19

138
0

Hukumar Lafiya a matakin farko ta tarayya ta ce tana shirin samar da rigakafin cutar Covid-19 tsakanin karshen watan Fubrairu zuwa farkon watan Maris na shekarar 2021.

Babban Daraktan hukumar Dr. Faisal Shuaibu, wanda ya bayyana haka lokacin da yake magana a wani taron wayar da kai tare da shugabannin kafafen yada labarai da masu tsara shirye-shirye, dangane samar da rigakafin Covid-19 a ranar Juma’a, ya ce rigakafin wani kwarin guiwa ne na yaki da cutar.

A wajen taron, wani shehin malami kan kwayoyin cuta masu yaduwa Farfesa Oyewale Tomori ya ce gwamnatin Nijeriya ba ta yin abun da ya kamata wajen yin gwajin masu cutar, saboda kasar ba ta da wadatattun kayan gwaji.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply