Home Labarai An bindige malamin Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Kebbi a Abuja

An bindige malamin Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Kebbi a Abuja

125
0

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani malamin jami’ar tarayya da ke Birnin Kebbi a jihar Kebbi, inda kuma suka ci gaba da harbe-harbe,

Daily Trust ta rawaito cewa an kashe marigayin mai suna, Abdullahi Abubakar Dakingari, a Abuja ya yin da ya ke kan hanyarsa ta dawowa daga ziyartar mahaifinsa da ke kwance a wani asibiti da aka kwantar da shi.

Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garinsu, Dakingari.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply