Home Coronavirus An buɗe makarantu a Jigawa, ma’aikata za su koma aiki

An buɗe makarantu a Jigawa, ma’aikata za su koma aiki

262
0

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, ya bada sanarwar buɗe makarantu 40 nan take, tare da umartar ɗaukacin ma’aikatan jihar su koma bakin aiki daga ranar 4 ga watan Agusta.

Gwamnan wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da ƴan jarida a birnin Dutse, ranar Litinin, ya kuma umarci ma’aikatun lafiya da na ilimi su fito da wani tsari da zai tabbatar ana bin ƙa’idojin kare kai da kamuwa da Covid-19.

Kamfanin dillancin labarun Nijeriya NAN, ya ruwaito cewa wannan mataki na zuwa ne makonni bayan ma’aikata daga mataki na 12 zuwa sama sun koma aiki.

Gwamnan ya ce dalilin ɗaukar matakin ma’aikatan su koma aikinsu ya zo ne bayan ci gaban da ake samu wajen yin biyayya ga matakan kariya daga kamuwa da cutar bayan ma’aikatan ƴan mataki na 12 sun koma aiki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply