Home Labarai An bude yakin neman zaben kananan hukumomi a Nijar

An bude yakin neman zaben kananan hukumomi a Nijar

49
0

Da misalin karfe sha biyun daren Talata wayewar Larabar nan ne a hukumance aka kaddamar da bude kyamfe na ‘yan takarar kananan hukumomi a zaben da ke tafe a fadin kasar Nijar.

Tuni dai manyan biranen kasar suka dauki harama inda ko ina ka duba, tutocin jam’iyyu ne suka mamaye manyan titunan biranen.

A ranar 13 ga wannan wata na Disamba ne dai za a gudanar da zaben kananan hukumomi domin ‘yan takarar nada kwanaki 10 na yakin neman zaben.

A ranar 5 ga wannan watan Disamba ne har ila yau za a bude yakin neman zaben na shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki ta kasa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply