Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi An cefanar da tashar lantarki ta Afam

An cefanar da tashar lantarki ta Afam

95
0

An gudanar da bikin cefanar da tashar samar da hasken lantarki ta Afam da gwamnatin tarayya ta yi ga ƴan kasuwa kan Naira Biliyan 105 a ranar Alhamis.

Taron wanda ya gudana a ofishin mataimakin shugaban ƙasa zai tabbatar da ƙarƙare cinikin tashar wutar da za a sayarwa kamfanin Transcorp Consortium.

A watan Oktoban shekarar 2019 ne dai majalisar kula da cefanar da kayan gwamnati ta amince da sayar da tashar lantarkin ga kamfanin a kan Naira Biliyan 105 da miliyan 300.

Wannan dai ɗaya daga cikin manyan matakan da Majalisar wadda Osinbajo ke jagoranta, ta ɗauka a taronta na biyu a ranar 14 ga watan Oktoba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply