Home Labarai An ceto amarya da angon da aka yi garkuwa da su a...

An ceto amarya da angon da aka yi garkuwa da su a Katsina

338
0

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da ceto karin mutane 37 da aka yi garkuwa da su, ciki kuwa ha da amarya da angon da aka yi garkuwa da su.

Mutanen da mafiyawansu mata ne da kananan yara, sun ce sun kwashe kwanaki 15 a hannun ‘yan bindiga.

Ango da amaryar wadanda ‘yan asalin kauyen Bakon Zabo ne na karamar hukumar Batsari jihar Katsina, sun ce sun sha bakar azaba a hannun wadannan ‘yan ta’adda.

Da suka nemi a sakaya sunayensu, sun ce a wurin da aka tsare su, ba su samun damar yin ibada Kuma abinci ma sau daya ake ba su a rana.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply