Home Labarai An ceto mutane 104 daga hannun ƴanbindiga a Katsina

An ceto mutane 104 daga hannun ƴanbindiga a Katsina

81
0

Gwamnatin jihar Katsina ta ce kimanin mutane 104 ne aka ceto bayan an sace su a jihar.

Gwamna Aminu Masari wanda ya bayyana haka, ya ce daga cikin mutanen 104, 16 sun fito ne daga karamar hukumar Sabuwa, Faskari da Dandume, 10 daga Danmusa sai kuma sauran 77 da suka fito daga karamar hukumar Batsari da Jibia.

Ya ce ceto mutanen ci gaba ne da wani aikin ceto wadanda aka sace wanda aka fara daga lokacin da aka sace dalibai 344 na makarantar sakandiren Kimiyya ta Ƙankara.

A nasa bangaren, kwamishinan ‘yansandan jihar Sanusi Buba ya shaidawa ‘yanjarida cewa daga cikin hanyoyin ceto mutanen sun hada yadda ‘yanbindigar da kansu ke neman zaman lafiya ta hanyar yin kiraye-kiraye daban-daban.

Daya daga cikin wadanda aka ceton Ado Umaru dan kimanin shekara 70 da aka sace tare da yaransa uku daga kauyen Wagini na karamar Hukumar Batsari, a fadi yadda suka sha wahala a hannun ‘yanbidigar na lisam sato biyu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply