Home Sabon Labari “An ci amanar siyasar gidan marigayi Sanata Mustapha Bukar a Katsina”

“An ci amanar siyasar gidan marigayi Sanata Mustapha Bukar a Katsina”

297
0

Ra’ayin Usman G Jibrin Funtua mazaunin Daura ba ra’ayin DCL Hausa ba

Usman G Jibrin

 

 

 

Marigayi Mustapha Bukar Tun kafin yazama sanata mutum ne mai arzuki shiyasa koda yatafi majalisar dattawa ba naiman Riga ko mota yakaishi majalisa ba domin Allah ya hore masa tun kafin ai daran akai kwandi.

Kowane Dan siyasa yanada committee committee da cincirundon masoya da masu hidimtawa hidimarsa,amma tunda wannan bawan Allah yakoma ga mahaliccinsa yaran gidan siyasarsa babu wani zababbe daya jawosu a jiki.

Ina zababbu daga state zuwa federal da masu rike da mukamin siyasa walh kujawosu sunada amfani idan kukai sakaci suka dunkule zasu Baku bakar wahala da hasarar kuri’u a kakar zaben kwaci kanka da kanka ta shekarar 2023.

Rubutuna baida alaka da iyalan wannan marigayi don su basu cikin lissafina a cin amanar da akai masu a siyasa.

Akwai wani daya jawosu a 2019 amma dabaici primary ba wukarsa takoma ma kubensa yayi wanchakali dasu to Allah kaimu 2023 insha Allahu zasu maida buki idan kuma an farga an gyara haka muke fata, don ma mutanen gidan siyasar madawaki basu da matattar zuciya suna noma kiwo aiki da naiman nakansu DSS…

Hankali yayi nazari da tunani a kana nan hukumomi goma sha biyu.

+DAURA
+SANDAMU
+MAI’ADUA
+BAURE
+ZANGO
+MASHI
+DUTSI
+MANI
+BINDAWA
+KANKIA
+KUSADA
+INGAWA

Ayi nazari dakyau a hankalta tun kafin wankin hula yakai dare,muna kara adduah ya Allah kajikan sen mustapha bukar Allah kakai rahama kabarinsa da iyayenmu baki daya.

Dan FUNTUA mazaunin Daura 2-December-2020

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply