Hukumar gudanarwar jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina ta sanar da cewa ta dage ranar rantsar da sabbin dalibai ‘yan aji 1 da biyu daga Litinin 1 ga watan Fabrairu, 2021 zuwa Alhamis 4 ga Fabarairu, 2021.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa daga Magatakardar jam’ar Malam Nasir Bello a Katsina.
Sanarwar tace kamar yadda aka sanar, lokaci da wurin da za a gudanar da bikin rantsuwar na nan ba su sauya ba, misalin karfe 9:00 na safe a babban dakin taro na jami’ar.
Sanarwar ta shawarci sabbin daliban da su je su amshi rigunan shan rantsuwa “academic gown” ta hanyar bin hanyoyin da suka dace.
