Home Labarai An dakatar da kwamashina saboda zargin yin lalata da budurwa

An dakatar da kwamashina saboda zargin yin lalata da budurwa

150
0

Bayan samun korafe-korafen jama’a, sakamakon zarginsa da neman yin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 16, mai suna Barakat Mayowa Melojuekun, Kwamishinan Muhalli na jihar Ogun Hon. Abiodun Abudu-Balogun, ya samu takardar dakatarwa daga gwamnatin jihar.

Jaridar Blueprint ta rawaito cewa a cikin wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar Ogun, Mista Tokunbo Talabi, ya fitar a jiya Lahadi ta ce dakatarwar da aka yi wa Mista Abudu-Balogun za ta taimaka wa rundunar ‘yansandan jihar wajen samar da kwararan hujjoji da ma muhimman bayanai na binciken da su ke yi.

Tuni dai, aka umurci Kwamishinan da aka dakatar, ya mika ragamar ma’aikatarsa ga babban sakatare, a ma’aikatar muhalli.

Talabi ya kuma ce, gwamnatin jihar za ta yi iya kokarinta don ganin an yi adalci akan wannan lamarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply