Home Labarai An damfari mai sayar da tabar wiwi da kudin jabu

An damfari mai sayar da tabar wiwi da kudin jabu

81
0

Abdullahi Garba Jani

Wani dilan tabar wiwi a birnin Legas ya jefa kanshi a tsaka-mai-wuya a dai dai lokacin da ya kira ‘yan sanda don su kama wasu masu sayen tabar a wajensa bisa zargin sun ba shi jabun kudi.

An zargi masu sayen tabar wiwin Sunday Uche mai shekaru 24, da Patrick Chidiebere mai shekaru 25 da yunkurin cutar mai sayar da tabar wiwin a inda suka ba shi kudi Naira dubu 21,500 kudin jabu.

Mai sayar da tabar wiwin da ba a ayyana sunansa ba, ya gayyaci ‘yansandan da ke sintirin “patrol” kan lamarin, wanda hakan ya jaza aka kama dukansu.

Jaridar Punch ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar 3 ga wannan watan na Disamba.

Matasan dai sun gurfana a gaban kotun Majastare da ke Yaba ta jihar Legas inda aka zarge su da ba da jabun kudi ga wanda suke sayen tabar wiwi a kasuwar Tejuosho.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply