Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta dauki karin likitici da sauran ma’aikatan lafiya 993 don shawo kan matsalar karancin ma’aikatan lafiya a asibitocin jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Engr Nuhu Yakubu Danja ya sanar da hakan a Katsina a taron bita ga ‘yanjarida kan cutar corona.
Kwamishinan ya ce an dauki nauyin likitoci 30 don zurfafa ilminsu a fannonin da suka shahara a ciki da wajen kasar don inganta kiwon lafiya a jihar.
