Home Labarai An fara gwanjon gwala-gwalan tsohuwar minista Diezani

An fara gwanjon gwala-gwalan tsohuwar minista Diezani

40
0

Kwamitin da aka kafa domin sayar da kayayyakin da gwamnatin tarayya ta kwace daga masu laifi ta fara sayar da wasu kadarori 25 a sassan kasar daban-daban.

Mr Daya Apata, Shugaban kwamitin ya sanar da hakan a jiya yayin taron manema labarai a birnin Tarayya Abuja.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ranar 9 ga watan Nuwamba na shekarar bara ya kafa kwamitin bayan ganin akwai bukatar hakan sannan ya umurci ofishin Ministan Shari’a na kasa ya saka ido kan ayyukan kwamitin na karbo kadarorin gwamnati da sayar da su.

Apata ya ce kwato kadarorin gwamnati da sayar da su na cikin ayyukan shari’a. Ya ce kwamitin yana da wakilai daga hukumomin tsaro da suka hada da, Yan sanda, Sojojin Ruwa, EFCC, ICPC da ma’aikatun kudi, shari’a, ayyuka da sauransu.

“Muryar ‘Yanci” ta rawaito cewa cikin kadarorin da za a sayar akwai filaye, masana’antu, injina, motoccin hawa, kayan ado kamar gwala-gwalai da sauransu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply