Home Labarai An fara shirin killace masu tabin hankali a Sokoto

An fara shirin killace masu tabin hankali a Sokoto

92
0

Mu’awuya Abubakar Saddiq

Wasu gamayyar hukumomi da suka hada na da Hisba, Zakka da wakafi, da kuma na jami’an tsaeon farar hula na “Civil Defence” sun soma aikin kamun masu fama da tabin hankali dake gara-ramba a titunan jihar Sakkwato.

Masu fama da tabin hankalin maza da mata ana kama su ne inda ake kai su assibitin masu tabin hankali da ke karamar hukumar Kware a jihar Sakkwato.

Duk mutum daya akan kashe masa akalla dubu arba’in da takwas na ci da sha da sauran dawainiya, sannan idan ya ji sauki a samar masa da sana’ar dogaro da kai.

A Birnin Sakkwato dai, akwai dumbin masu fama da tabin hankali da galibi wasu ke alakantawa da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply