Home Labarai An farmaki ofishin ƴan sanda, an kashe jami’ai biyu a Edo

An farmaki ofishin ƴan sanda, an kashe jami’ai biyu a Edo

96
0

Rahotanni daga jihar Edo na cewa wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a shelkwatar ‘yan sanda da ke Igueben, ta jihar Edo, inda suka kwashe dimbin makamai da alburusai tare da jikkata jami’an‘ yan sanda biyu da suke a bakin aiki.

Jami’an ‘ƴan sandan biyu da lamarin ya rutsa da su, akwai mai mukamin Sufeta ɗayan kuma Kofur, an garzaya da su wani asibitin jihar domin yi masu magani.

Sai dai kuma karin jami’an yan sanda biyu sun mutu yayin harin, inda tuni aka tura gawarwakinsu a dakin ajiye gawa.

Sai dai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor, ya ce jami’ansu biyu da suka samu rauni suna nan a raye.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply