Home Labarai An gano ma’aikatan INEC biyu da suka ɓace a zaɓen Zamfara

An gano ma’aikatan INEC biyu da suka ɓace a zaɓen Zamfara

137
0

An gano Ma’aikatan wucin gadi guda biyu da hukumar zaben INEC ta ayyana sun bace a lokacin zaben cike gurbi na mazabar Bakura a jihar Zamfara, ranar Asabar.

Daraktan wayar da kan masu zabe da yada labarai Nick Dazang ya bayyana haka a ranar Litinin, yana cewa ma’aikatan sun gudu ne don ceton rayukansu kuma suka bace hanya.

A ranar Lahadi ne dai, Kwamishinan zaben hukumar kan yada labarai da wayar da kan masu zabe Festus Okoye, ya ayyana zaben cike gurbin a matsayin wanda ba kammalalle ba saboda banbancin kuri’u 2,181 da ke tsakanin ‘yan takatar jam’iyyar PDP da na APC bai kai yawan masu rajistar zabe da ake da su a rumfunan zabe 14 da aka soke zabukansu, da suka kai 11,429 ba.

Ya ce hukumar ta zauna tare yanke hukuncin kammala zaben a ranar Laraba 9 ga watan Disamba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply