A kammala saukar karatun Al-Qur’ani mai girma da addu’o’i a jihar Kebbi domin neman kariya daga ambaliyar ruwa dama rashin tsaro da ya addabi wasu sassan kasar nan.
Malam Yahaya Sarki wanda shi ne bai wa gwamnan jihar ta Kebbi Alhaji Atiku Bagudu shawara kan kafafen yada labarai ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka rarraba ga manema labarai a jihar.
Ya ce an shirya karatu da addu’o’in ne domin neman gafarar Allah madaukakin sarki ya ceto jihar da ma kasa baki daya daga annobar iftila’in ambaliyar ruwa da kuma rashin tsaro.
