Home Addini An gudanar da sallar Juma’a a Hagia Sophia

An gudanar da sallar Juma’a a Hagia Sophia

175
0

Al’ummar Muslimi sun gudanar da sallar Juma’a a karon farko a dadadden ginin nan na Hagia Sophia da aka mayar da shi masallaci a birnin Santanbul na kasar ta Turkiya.

Shugaban kasar Turkiya Racep Tayyib Erdogan na daga cikin wadanda suka halarci sallah a masallacin ya kuma karanto wasu ayoyi daga cikin Alqur’ani mai girma domin nuna farin cikinsa.

Sai dai magoya bayan shugaban kasar masu ra’ayin yan mazan jiya sun fara bayyana cewa Erdogan na son mayar da tsarin mulkin kasar irin na musulunci.

A baya dai, wurin coci ce, sai ya koma masallaci, daga nan ya rikide ya koma wurin adana kayan tarihi, sai yanzu kuma aka mayar da shi masallaci. Wannan lamarin ya faru ne cikin shekaru 1500.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply