Home Labarai An hana shugaban jami’ar Legas shiga harabar jami’ar

An hana shugaban jami’ar Legas shiga harabar jami’ar

203
0

Kungiyar Malaman jami’a (ASUU) reshen jami’ar jihar Legas hadin guiwa da kungiyar ma’aikatan jami’ar sun toshe babbar hanyar shiga harabar jami’ar jihar Legas (LASU), sakamakon rashin biyansu ariyas na karin albashi.

Ya yin da kungiyoyin su ke gudanar zanga-zangar, sun hana shugaban jami’ar, Farfesa Olanrewaju Fagboun, shiga jami’ar har sai ya bayyana masu halin da ake ciki dangane da rashin biyansu kudaden ariyas nasu na mafi karancin albashi da gwamnati ta bayyana cewa ta yi.

Yau ne dama ake sa ran bude makarantun gaba da sakandare a jihar kamar yadda gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya bayyana, tun bayan kulle su da aka yi sakamakon bullar annobar corona.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply