Home Labarai An hana wasu likitoci fita daga Nijeriya

An hana wasu likitoci fita daga Nijeriya

116
0

Hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya ta dakatar da wasu likitoci su 58 ya yin da suke kokarin ficewa daga kasar zuwa kasar Birtaniya.

Mr Sunday James shi ne mai magana da yawun hukumar ya ce hukumar ta dakatar da wadannan likitoci a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Mr Sunday ya kara da cewa hukumar ta hana jirgin da ya zo daukar wadannan likitocin da ke son zuwa kasar Birtaniya domin su halarci wani shirin horaswa ne sakamakon ba su da takardar izinin shiga kasar.

A karshe ya ce tuni jirgin da ya zo daukar wadannan likitoci ya koma ba tare da ya dauke su ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply