Home Labarai An horas da manoma da makiyaya kan zaman lafiya a Kebbi

An horas da manoma da makiyaya kan zaman lafiya a Kebbi

19
0

Shirin bunkasa harkokin noma na tarayya reshen jihar Kebbi da Sokoto ATSPS1, ya kaddamar da wani taron horaswa na kwanakki uku ga namoma da makiyaya kan yadda za a bunkasa sha’anin noma da kiyo, wanda ya gudana a cikin Birnin Kebbi

A jawabinsa shugaban shirin na kasa Ibrahim Muhammad Arabi, wanda Adekunle Alabi ya wakilta, ya bayyana cewa dalilin shirya wannan horo shi ne, domin ilmantar da manoma yadda za su inganta sha’anin noma da kiyo.

Ya kara da cewa za su ci gaba da horas da manoman kan samar da abinci kala daban-daban da kuma yadda za a rika magance rikici tsakanin manoma da makiyaya.

A nasa jawabin shugaban shirin na yankin Kebbi da Sokoto, Malam Aliyu Abubakar Dogon Daji, ya ce kananan hukumomi takwas ne suka halarci taron, bakwai daga ciki sunfito daga jihar Kebbi sai daya daga jihar Sokoto, kuma za a dauki kwana uku ana gudanar da horon.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply