Home Labarai An jibge jami’an tsaro 302 don yaƙi da ƴanbindiga a Kaduna

An jibge jami’an tsaro 302 don yaƙi da ƴanbindiga a Kaduna

45
0

Gwamnatin Nijeriya ta jibge dakarun ‘yansandan kwantar da tarzoma 302 domin yaki da ‘yanbindigar da suka addabi jihar Kaduna.

Da yake kaddamar da dakarun tsaron, Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, ya ce jihar na fama da ayyukan ‘yanbindiga, satar mutane da shanu, da kuma fashi da makami na tsawon lokaci.

Gwmnan wanda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya wakilta, ya bukaci jami’an tsaron su yi aiki tukuru wajen tabbatar da dorewar nasarar da ake samu wajen dawo da zaman lafiya a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa za a jibge jami’an ne a yankunan Birnin-Gwari, Giwa, Igabi, Chikun da Kajuru, masu fama da matsalolin tsaro domin samar da zaman lafiya.

A nasa jawabin, kwamishinan ‘yansandan jihar Umar Muri, ya ce yawaitar makamai a hannun jama’a ba bisa ka’ida ba, na daya daga cikin abubuwan da ke kara ta’azzara matsalar tsaro a jihar da ma kasa baki daya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply