Home Coronavirus An kaddamar da Askarawan yaƙi da Covid-19 2,000a Kano

An kaddamar da Askarawan yaƙi da Covid-19 2,000a Kano

37
0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da Askarawan COVID-19 su 2,000 don wayar da kan al’umma tare da tabbatar da bin ka’idojin kariya daga cutar a fadin jihar.

Shirin na daga cikin kokarin gwamnatin don ganin an dakile yaduwar cutar a zagaye na 2 kasancewar cutar ta fi yaduwa a yanzu fiye da karon farko a jihar.

Yayin kaddamar da askarawan a gidan gwamnatin jihar, Gwamnan ya ce duk da ba za a sake rufe jihar ba amma gwamnati ba za ta zuba idanu ganin ana karya ka’idojin kariyar cutar ba, a don haka ne aka kirkiri Askarawan don taimaka wa jami’an tsaro wurin yaki da yaduwar cutar.

Da yake maida jawabi shugaban kwamitin yaki da cutar ta COVID-19 Tijjani Ibrahim ya kirayi al’umma da su ci gaba da bada hadin kai wajen bin ka’idojin kariya, yana mai jaddada cewa zagayen na 2 ya fi na farkon da ya gabata hadari, ya shaida cewa a cikin duk mutum 100 da aka yi wa gwajin ana samun 13 dauke da cutar.

Mai martaba sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa kokarin da take na ganin ta tsare lafiyar al’ummarta, ya kuma kirayi mutane da su bada hadin kai tare da bin ka’idojin kariya daga cutar ta Coronavirus.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply