Home Labarai An kafa asibitin wucin gadi a Madina domin alhazan Nigeria

An kafa asibitin wucin gadi a Madina domin alhazan Nigeria

174
0

Hajjin 2019: AN KAFA ASIBITIN WUCIN GADI A MADINA DOMIN ALHAZAN NAJERIYA

Shugaban kwamitin kula da lafiyar alhazan Najeriya Dakta Ibrahim Khana ya shaidawa mujallar www.hajjreporters.com cewa likitico da sauran jamian kiwon lafiya su 256 ne za su yi aiki a sabon asibitin alhazan Najeriya da aka bude a birnin Madina.

Baya ga wannan asibiti acewar shugaban likitocin, gwamnati ta tanadi wurin bada taimakon gaggawa ga marasa lafiya a dukkanin masaukan alhazai. 
Burin dai shi ne a kula da lafiyar alhazan Najeriya komi kankantar cutar da za ta kama Alhaji.

A ganin wannan mataki zai iya samar da kulawar likita ga alhazan Najeriya?

#RiT

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply