Home Coronavirus An kafa dokar hana fita a Sokoto bayan mutum 8 sun mutu...

An kafa dokar hana fita a Sokoto bayan mutum 8 sun mutu silar Covid-19

216
0

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ce yanzu haka an samu mutum 66 da suka kamu da cutar Covid-19 yayin da 8 suka mutu a jihar.

Tambuwal wanda ya bayyana haka a lokacin wani jawabi a kafafen yaɗa labarai ya ce wannan adadi ya sanya jihar Sokoto shiga sahun gaba gaba na jerin jihohin da cutar ke yaɗuwa a Nijeriya.

Ya yi bayanin cewa ganin yadda al’amura ke ƙara tsananta, akwai ƙarin matakai da za a ɗauka a matakin jiha da na tarayya don daƙile yaɗuwar al’amarin.

A kan haka, gwamnan ya saka dokar hana fita a jihar da za ta fara aiki daga misalin ƙarfe 8:00pm na daren yau Litinin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply