Home Labarai An kafa kwamitin binciken rikicin jami’ar Legas

An kafa kwamitin binciken rikicin jami’ar Legas

123
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada kwamitin da zai gudanar da bincike da ma yin sasanci akan rikicin jami’ar jihar Legas.

An dai ba kwamitin wa’adin makonni biyu da ya gaggauta kammala binciken tare da aike da rahotonsa na shawarwari bayan kammala binciken.

Tuni dai ma’aikatar ilimi ta tarayya ta umurci uban jami’ar Wali Babalakin da shugaban jami’ar Farfesa Oluwatoyin Ogundipe da su dakatar da ayyuka a lokacin da kwamitin zai ziyarci jami’ar.

Farfesa Dikko Sa’ad ne zai jagorancin kwamitin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply