Home Labarai An kai wa kungiyar kwallon kafa ta Adamawa United hari

An kai wa kungiyar kwallon kafa ta Adamawa United hari

26
0

‘Yan bindiga sun hari kungiyar kwallon kafa ta Adamawa United FC, a yayin da suka sace direban motar a kan babban titin Benin-Ore a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa wasan Firimiyar Nijeriya mako na 11.

DCL Hausa ta gano cewa ‘yan wasan na kan hanyar su ta zuwa Lagos domin karawa da kungiyar kwallon kafa ta MFM.

Bayanai sun ce an yi wa ‘yan wasan kwacen wayoyinsu, kudade da sauran abubuwan amfani.

Wani dan wasa mai suna Sadiq Lawan, yace lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na daren Juma’a wayewar Asabar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply