Home Labarai An kama ‘ƴar bautar kasa bisa zargin ta kashe saurayinta

An kama ‘ƴar bautar kasa bisa zargin ta kashe saurayinta

147
0

Rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen jihar Akwa Ibom ta ce ta yi nasarar cafke wata matashiya ƴar bautar kasa mai suna Chidinma Oduma Pascaline, da ake zarginta da kashe saurayinta.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Odiko Macdon, ne ya tabbatarwa da manema labarai kamun da aka yi wa Chidinma.

Matashiyar mai kimanin shekaru 26, an bada rahoton cewa ta kashe saurayinta mai suna, Akwaowo Japhet har lahira a ranar Lahadin da ta gabata.

Chidinma ta shiga hannu ƴansanda a daidai lokacin da take kokarin tserewa daga gidan saurayin nata bayan faruwar lamarin.

To sai dai tuni Kwamishinan ’yansandan jihar, Andrew Amiengheme, ya bada umurnin a gudanar da bincike cikin tsanaki game da faruwar lamarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply