Rundunar ƴansandan jihar Kebbi ta kama wasu ɓarayi guda huɗu da ake zargi da ƙwacen babura a ƙananan hukumomin Birnin Kebbi da Jega.
Kakakin rundunar DSP Nafi’u Abubakar wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya aikewa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN, ranar Juma’a, a Birnin Kebbi, ya ce waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu.
Ya ƙara da cewa a ranar 19 ga watan Janairu, jami’an rundunar Puff Adder dake sintiri a Bena/Mairairai a ƙaramar hukumar Danko-Wasagu sun kama wani matashi da wata ƙaramar jaka, kuma da aka bincika, an samu alburusai 107 a ciki.
Ya ce tuni Kwamishinan ƴansandan jihar ya bada umurnin tura su sashen binciken laifuka CID, domin ci gaba da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.
