Rundunar ƴansanda reshen jihar Benuwe ta ce ta kama wani matashi mai suna Jeremiah Nnamdi, dalibi a jami’ar gwamnatin tarayya ta aikin gona da ke Makurdi kan zarginsa da kisan malaminsa Farfesa Karl Kwaghger.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Catherine Anene, ta fitar a ranar Asabar.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya rawaito cewa an kashe Farfesa Karl Kwaghger ne a ranar 28 ga Nuwamban nan a wurin shakatawa na gidauniyar Tarka, Gboko.
Rundunar ƴansandar ta ce ta yi nasarar kama wanda ake zargin dan asalin jihar Imo ne a Abuja yayin da yake kokarin sayar da motar marigayin.
