Home Addini An kama boka mai yi wa mata wankan tsarki a Kano

An kama boka mai yi wa mata wankan tsarki a Kano

510
0

Hukumar Hisba reshen jihar Kano ta kai wani samame a yankin karamar hukumar Dawakin-Kudu inda ta yi nasarar cafke wani boka da ake zargi da yi wa matan aure wankan magani.

Mutumin da aka bayyana sunanshi da Usman dan kimanin shekaru 30 ya shiga hannun hukumar ne a daidai lokacin da ya ke tsaka da yin wani aiki.

Usman da ya ke fake wa cewa yana da rauhanai da suke taimaka masa wajen yi wa mata maganin matsalolinsu, rediyo Nijeriya Kaduna ya samu damar zanta wa da shi ya kuma bayyana cewa “an same shi yana tsaka da yin aikin magani, a wani gida da aka kirashi sai ga jami’an hukumar hisba inda sukayi ram da ni ” inji Usman.

A nasa bangaren shugaban hukumar ta hisba Ustaz Sheikh Sani Ibn Haroun ya bayyana cewa an sami Boka Usman tare da kundin tsatsubarsa.

Ustaz Ibn Haroun ya ce babban abin da ya fi tayar masu da hankali shi ne yadda matan aure ke alaka da wannan boka da sunan zuwa wajensa neman magani, har ta kai ga yana masu tsirara da nufin yi masu wankan magani.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply