Home Labarai An kama Ɗansanda da safarar kananan yara

An kama Ɗansanda da safarar kananan yara

93
0

Jami’an Hisba na jihar Kano sun kama wani kwanstabul na ƴansanda bisa zargin safarar yara ƴanmata da kuma huldar masha’a.

Ɗansandan da aka bayyana sunansa Basiru da abokin barnar tasa Jamilu, suna amfani da wani gida a yankin Rummawa dake karamar hukumar Ungogo wajen rudar yaran matan zuwa ga wannan badalar.

Dubun Basiru ta cika lokacin da mutanen yankin suka sanar da jami’an Hisba bayan ya shigar da wata yarinya yar kimanin shekara 16 a cikin gidan.

Wani Jami’in Hisba daya bukaci a sakaya sunansa ya shaida cewa dama sun sha karbar korafe-korafe akan wannan gida da barnar da ake aikatawa a ciki, har zuwa yanzu da dubu ta cika.

Ya zuwa yanzu dai Jami’an Hisba sun miƙa su a hannun Jami’an ƴansanda domin ci gaba da bincike.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply