Home Labarai An kama mai satar ɗan kamfan mata a Ogun 

An kama mai satar ɗan kamfan mata a Ogun 

183
0

Rundunar ƴan sanda reshen jihar Ogun ta kama wani saurayi ɗan shekara 16, Adeniyi Muhammed bisa zargin satar nau’ika daban-daban na ɗan kamfan mata.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar jihar, Abimbola Oyeyemi ya fitar a Abeokuta, ta ce an kama wanda ake zargin ne bayan wani mutum mai suna Amudalat Opaleye, mazaunin titin Kano da ke Ayetoro, ya kawo ƙorafin matashin, a ofishin ƴan sanda na yankin.

Tuni dai, kwamishinan ƴan sandan jihar Edward Ajogun ya ba da umarnin a tura matashin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar domin a ci gaba da gudanar da bincike.

Satar ɗan kamfai na ɗaya daga cikin abun da yake ci wa matan kudancin Nijeriya tuwo a ƙwarya musamman a wannan lokaci da abu ke ƙara ta’azzara.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply