Home Labarai An kama masu casun tsiraici a Bauchi

An kama masu casun tsiraici a Bauchi

52
0

Ƴansanda a jihar Bauchi sun kama gungun wasu matasa 19 da suka shirya casun tsiraici a jihar.

Dubun bata-garin masu shekaru 19 zuwa 22 ta cika ne bayan sun shirya sharholiyar ta su a karamar hukumar Dass ta jihar Bauchi.

Kakakin rundunar ƴansandan jihar, DSP Ahmed Mohammed Wakil ya ce bayan samun bayan sirri ne rundunar ta fara aiki ba dare ba rana domin kawo karshen gungun bata-garin.

Ya kara da cewa gungun matasan sun addabi jama’ar Dass da kwacen waya da sauran nau’uka na fitsara ciki har da gudanar da casun tsiraici.

DSP Lawal ce kwamishinan ƴansandan jihar, CP Lawan Tanko Jimeta, ne da kansa ya tura tawagar rundunar kar-ta-kwana (RRS) domin cafko su.

Ya ce bayan kammala binciken matasan da shekarunsu bai haura 22 ba za a gurfanar da su a gaban kotu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply