Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta ce ta yi nasarar kama mutane hudu da ake zargi da bi gida-gida suna fashi da makami a jihar.
A cikin wata takarda daga mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Sulaiman Yahaya Nguroje, wace DCL Hausa ta karanta rundunar ta ce an kama wadanda ake zargin ne a yankin karamar hukumar Girei ta jihar.
Takardar ta ce matasan masu shekaru 21, 23, 22 da 23 na harar mutane a cikin gida a yankin Sangere Futy inda suke amfani da muggan makamai a wajen gudanar da ayyukan nasu.
Nguroje yace an kwato wayoyin hannu, layukan waya, kwanfitoci da na’urar sanyaya daki ta “AC” sannan za a gurfanar da su gaban kulya don girbar abin da suka shuka.
Labarai masu alaka:
‘Yansanda sun bindige dan fashi da makami a Katsina
Maigadi ya yi hayar ‘yan daba don yi wa maigidansa sata
