Home Labarai An ceto mutane 393 daga hannun masu garkuwa da mutane a Katsina...

An ceto mutane 393 daga hannun masu garkuwa da mutane a Katsina cikin 2020

78
0

Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta hannun kwamishinan ‘yansandan jihar Sanusi Buba ta ce jami’anta sun sun kubutar da jimillar mutane 393 daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar cikin shekarar 2020.

A taron manema labarai na karshen shekara 2020 da ya gudanar a Katsina, Sanusi Buba yace ‘yansanda sun kuma kama mutane 304 da ake zargi da sata da garkuwa da mutane a jihar.

Yace ‘yansanda sun kuma hallaka ‘yan ta’adda 29 a musayar wuta da suka yi da su a cikin shekarar 2020 a jihar.

Yace ‘yansanda sun kuma yi nasarar kwato bindigu samfuri daban-daban har 57 da alburusai masu rai 600 daga ‘yan ta’adda a jihar cikin 2020.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply