Home Labarai An kama shi da kokon kawunan mutane hudu

An kama shi da kokon kawunan mutane hudu

222
0

Jami’an rundunar ‘yansanda a jihar Ogun sun kama wani mutum mai shekara 55, Yesiru Salisu da ke zaune a yankin Ijebu Igbo da ke jihar bisa mallakar kokon kawunan mutane guda 4, busassun hannayen mutum biyu da kuma muƙa-muƙin mutane uku a cikin jakarsa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abimbola Oyeyemi ne ya sanar da haka ya yin zantawarsa da manema labarai a Abeokuta a Larabar nan.

 

Sai dai tuni kwamishinan ‘yansanda na jihar ta Ogun Edward Awolowo Ajogun ya ce ya ba da umurnin a gaggauta mika wannan magidanci zuwa ga sashen binciken manyan laifuka na jihar don ci gaba da bincike da ma yi masa hukuncin da ya dace.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply