‘Yansanda a Kano sun ce sun kama mutumin mai suna Haruna Ya’u da aka zarga da kashe abokinsa Musa Muhammad bayan musayar yawu kan 500.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Abdullahi Haruna ne ya tabbatar da hakan a lokacin da tattaunawarsu ta wayar tarho da jaridar Punch.
An zargi Haruna da soka wa Muhammad mai shekaru 18 almakashi a unguwar Dantsinke da ke karamar hukumar Tarauni jihar Kano.
