Home Coronavirus An kama shugaban ƙaramar hukuma da zargin karkatar da kayan tallafin Covid-19...

An kama shugaban ƙaramar hukuma da zargin karkatar da kayan tallafin Covid-19 a Kano

168
1

Hukumar sauraron koken jama’a da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano, ta kama shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso Kabiru Ado Panshekara bisa zargin nuna ƙarfin iko tare da karkatar da kayan talaffin Covid-19.

Shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimingado ya tabbatar da kamun Panshekara ga ƴan jarida a yau Asabar.

Hukumar ta ce shugaban ƙaramar hukumar, ya raba kayan tallafin ga jami’an tsaro irin su ƴan sanda, DSS, jami’an shige da fice da na Hisbah, da dai sauran su.

Hukumar ta ce wannan ya saɓawa sashe na 22, 23 da 26 na dokar hukumar ta shekarar 2008 da akaiwa gyaran fuska.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply