Home Uncategorized An karrama wata marubuciya a Katsina

An karrama wata marubuciya a Katsina

187
0

A ranar Juma’ar makon nan ne mujallar zauren marubuta ta miƙa shaidar karramawa ga marubuciya Fatima Usaini El-ladan a ofishinta na Arewa “Live Media Trust Nig Ltd” da ke a Lambun Khadija, a birnin Katsina.

Ta samu karramawar ne a matsayin mai ba da gudummuwa da sadaukar da kai a harkar rubuce-rubuce.

Fatima ta rubuta litattafai da dama waɗanda suka haɗa da:
‘Yar talla, Baƙar mace, Tufka da warwara, Kowa Ya Sayi Rariya, Jinin Mahaifina, Riƙon-Kaka, Mazan ko Matan, da dai sauransu da dama.

Fatima ta yi fice wajen rubuta labaran da za su warware matsaloli ko kawo zaman lafiya a cikin al’umma.

A jawabinta na godiya, ta yi godiya matuƙa ga Mujallar Zauren Marubuta bisa ga wannan karramawa da ta samu, ta kuma nuna cewa ashe duk abin da mutum ya ke yi mutane suna gani, tun da saboda ƙoƙarinta da Mujallar ta gani ta karrama ta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply