Home Sabon Labari An kasa rada wa jariri suna bayan an haife shi ta hanyar...

An kasa rada wa jariri suna bayan an haife shi ta hanyar yi wa mahaifiyarsa fyade

483
0
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Citizens United for Peace and Stability (CUPS), ta fitar da karin bayanai a kokarinta na ganin an hukunta mutumin da ya yi wa ‘yar shekaru 13 fyade a yankin Kafin Hausa na jihar Jigawa. Shugaban kungiyar CUPS Dakta Idris Ahmed ya wallafa wannan bayanin a shafinsa na Facebook:
Jama’a ga karin bayani, akan halin da yar shekara 13, wanda aka yi mata fyade da ciki, a Jihar Jigawa. Hajiya Ruqayya Madachima tayi hira da iyayen ita yarinyar. Daga bisani kuma tayi hira da ita yarinyar, Sha’awa.
1. Mun tabbatar cewa shi Idiyo wanda yayi wa Sha’awa fyade, kuma ya bata ciki, ashe ba saurayi bane. Shi dai magidanci ne, mai mata da yara 6!
2. A lokacin da Idiyo ya yi wa Sha’awa fyade da ciki, shekarunta 12 ne kacal.
3. Sha’awa ta haifi da namiji.
4. Har yanzu ba’a rada wa yaron suna ba, domin shi Idiyo yaki ya yarda da laifin da ake tuhumarsa da shi.
5. Idiyo yana ta yunkurin amfani da sanayyar da yake da ita a wajen mahukunta, domin kashe maganan.
6. Kungiyar kwato hakkin bil’adam, wato Citizens United for Peace and Stability (CUPS), ta lashi takobin samarwa Sha’awa hakkinta a kotu.
Zamu ci gaba da baku karin bayani nan gaba. Insha’Allah.
Dr. Idris Ahmed.
CUPS.
25/06/2020.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply