Ƙasar Panama 🇵🇦 ta kasafta lokutan fita waje tsakanin mata da mazan ƙasar.
A ranakun Litinin, Laraba da Juma’a, mata ne kaÉ—ai aka bari su fita don yin cefane.
A ranakun Talata Alhamis da Asabar kuwa, maza ne aka ba dama su fita don neman abun miya.
A ranakun Lahadi kuwa, babu wanda aka ba damar ya fito daga gidan sa.
Wannan doka da ta fara aiki a ranar Laraba, za ta shafe tsawon kwanaki 15 a ƙasar ta Panama 🇵🇦.
