Home Labarai An kashe Ƴanjarida sama da 50 a shekarar 2020 – Bincike

An kashe Ƴanjarida sama da 50 a shekarar 2020 – Bincike

112
0

Aƙalla ƴanjarida sama da 50 da suke bakin aiki aka kashe a shekarar 2020 mafiya yawansu a kasashen da ba su a cikin yake-yake.

Kididdigar ta bayyana mafi yawan ƴanjaridar da aka fi kai wa harin sun hada da masu bincike kan badakalar laifuka, cin hanci da rashawa da kuma sauran rigingimu.

Binciken ya bayyana kashe-kashen a Mexico, India da kuma Pakistan.

Kashi 84% na cikin wadanda aka kashe a wannan shekarar an farmakesu ne kai tsaye saboda aikinsu idan an gwada da kashi 63% na shekarar da ta gabata.

Babban editan jaridar RSF, Pauline Ades-Mavel ya bayyana cewa tsawon shekaru ƴanjarida masu binciken kwakkwafi na aikinsune akan tsini.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply