Gwamnatin jihar Gombe ta ce ya zuwa yanzu ta kashe kudaden da yawansu ya kai kimanin naira milyan dubu daya wajen yakar cutar corona a jihar.
Gwamnan jihar, Alhaji Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan, ya yin bikin kaddamar da wani sabon dakin gwaje-gwajen cututtuka da aka gina akan kudi โฆ miliyan 120 a cikin asibitin kwararru na jihar, Gombe.
Gwamna ya kara da cewa a yanzu haka jihar ta shirya tsaf wajen yakar kowace irin cuta, sannan ya kuma nuna cewa wannan sabon wajen gwaje-gwajen zai taimaka matuka wajen yakar annobar corona da ta addabi Duniya.
