Gwamnatin Nijeriya ta kashe kudade da suka kai kimanin Naira tiriliyon daya wajen biyan kudin ruwa da kuma wasu basussuka da suke kan ta.
Wadannan kudade dai an kashe su a tsakanin watan Janairu zuwa watan Mayun shekarar nan.
Ministar kasafin kudi da tsare-tsaren kasar ce ta bayyana haka a ya yin wani taro da aka gudanar dangane da bin ba’asin yadda ake kashe kudade da aka gudanar a Abuja.
