Home Coronavirus An koma karatun boko a Wuhan, inda Corona ta samo asali

An koma karatun boko a Wuhan, inda Corona ta samo asali

165
0

Akalla dalibai milyan daya da rabi sun koma makarantu a Talatar nan domin ci gaba da karatu a birnin Wuhan na kasar China inda cutar corona ta samo asali.

Birnin na Wuhan dai shi ke da kaso 50 cikin 100 na yawan mutanen da suka mutu sakamakon annobar ta corona.

Hukumomi a kasar sun bayyana cewa ya zama wajibi daliban su bi dokokin da ma daukar matakan kariya domin kauce wa sake bullar annobar.

A nata bangare, gwamnatin kasar ta ce akwai yiwuwar a fara ba da darussa daga gida idan har aka sake samun bullar cutar a karo na biyu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply