Home Labarai An kona ofishin ‘yansanda a Katsina

An kona ofishin ‘yansanda a Katsina

277
0

Wasu fusatattun matasa a garin Daddara na karamar hukumar Jibia a jihar Katsina, sun kona ofishin ‘yansandan da ke kauyen.

Matasan da suka fito zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu dangane da halin tsaron da yankunansu ke fuskanta, sun kona tayoyi a bisa titi tare da hanyar zuwa Jibia daga Katsina.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun yi nasarar kama mutane 43 daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifin.

Gambo Isah yace a cikin ofishin ‘yansandan da matasan suka kona, hada bindigu da motoci. Ya kara da cewa za a gurfanar da su gaban kotu domin girbar abin da suka shuka.

Ya yi kira ga jama’a da su rika ba jami’an tsaro hadin kai wajen gudanar da ayyukansu ta yadda za a gudu tare a tsira tare.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply